Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta bayyana ranar Talata cewa, matsalar rashin tsaro da aikin kakkabe masu tada kayar baya a arewa maso gabashin kasar Najeriya ya yi sanadin kaurar dubban jama'a, inda a yanzu haka sama da dubu 6 sun tsere zuwa kasashe dake makwabtaka da ita, in ji mai magana da yawun MDD yayin jawabinsa ga 'yan jarida.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, in ji mai magana da yawun magatakardan MDD Martin Nesirky, ta bayyana cewa mafi yawan mutanen da suka kaura mata ne da yara kanana don kare lafiyarsu a kasar Nijar.
Nesirky ya ci gaba da cewa, akasarin wadanda hukumar ta zanta da su sun bayyana cewa sun gudu ne saboda kada tsautsayi ya fada kansu a aiki da ake yi na kakkabo masu tada kayar baya dake da alaka da kungiyar Boko Haram.
A fadin hukumar ta UNHCR, kasar Nijar ta karbi 'yan gudun hijra guda 6240, da suka kunshi 'yan Nijeriya 2692, 'yan Nijar dubu 3544 da suka gudo kasarsu da kuma 'yan wasu kasashe guda 94, mafi yawansu 'yan kasar Chadi. Da zarar sun samawa iayalansu matsuguni a Nijar, mazan su kan koma Najeriya don yin aiki da yi wa iyali hidima.
Nesirky ya lura cewa, hukumar kula da 'yan gudun hijran ta kuma ga wadanda suka gudu zuwa kasashen Kamaru da Chadi a cikin 'yan makwannin nan.
Yace akwai mutane 155 daga Najeriya dake neman mafaka a Chadi tare da 'yan asalin kasar Chadi 716. Kana a kasar Kamaru, akwai 'yan kasar 1200 da suka komo.
A halin da ake ciki, ana cikin mawuyacin yanayi a Najeriya. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ba ta isa wasu sassan arewa maso gabashin kasar Najeriya ba saboda dokar ta baci, don haka babu cikakken bayani kan yanayin bil adama a arewa maso gabashin kasar.(Lami Ali)