in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya amince da kafa sabuwar tawaga a Somaliya
2013-05-03 10:40:52 cri

Kwamitin tsaro na MDD ya amince da kafa wata sabuwar tawaga, da za ta mai da hankali ga ba da agaji da taimako a kasar Somaliya. Tawagar wadda aka yi wa lakabi da UNSOM, za ta gudanar da ayyukanta a kasar ta Somaliya ne tsahon shekara guda a karon farko.

Kudurin kafuwar wannan tawaga da ya samu amincewar daukacin wakilan kwamitin 15, ya kuma yadda da kaddamar da UNSOM din ranar 3 ga watan Yunin shekarar 2013, karkashin jagorancin wakilin musamman na babban magatakardar majalissar dinkin duniya.

Har ila yau, an amince wa kwamitin tsaron majalissar, da ya nazarci kudurin da ya kafa wannan tawaga ta UNSOM, kafin ranar 30 ga watan Afrilun shekarar 2014 mai zuwa. An kuma amince da Nicholas Kay, ya zamo jagoran wannan tawaga da za ta zamo a babban birnin kasar Somaliyan wato Magadishu. Kay zai maye gurbin Augustine Mahiga, kuma ofishinsa zai rika gudanar da ayyukan tsare-tsaren manufofin MDD, wadanda za su baiwa gwamnatin Somaliya tallafi ga aikin wanzar da zaman lafiya da sulhunta bangarorin da suke adawa da juna.

A ranar 6 ga watan Maris ne dai kwamitin tsaron MDD ya amince da wani kuduri, na kara wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta AMISOM da shekara guda, sa'an nan aka sassauta takunkumin shigar da makamai kasar ta Somaliya, takunkumin da ya shafe shekaru 20 ana aiwatar da shi.

Har ila yau, kwamitin ya amince da ra'ayin babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon cewa, tawagar harkokin siyasar majalissar mai aiki a Somaliya UNPOS, ta kammala aikinta a tsahon shekaru 15, don haka, akwai bukatar a rushe ta, tare da maye gurbinta da wata sabuwa, da za ta aiwatar da wasu sabbin ayyukan ba tare da wani bata lokaci ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China