Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun cimma wata yarjejeniya a ranar Alhamis a birnin Khartoum, hedkwatar kasar Sudan kan batun shawarwarinsu na fara jayo man fetur a kasar Sudan ta Kudu da kuma fitar da shi zuwa kasashen waje ta hanyar ratsa kasar Sudan, duk da cewa, bangarorin biyu ba su tsai da da ranar fara wannan aikin ba.
An samu umurni daga bangarorin biyu domin ganin kamfanonin hakar man fetur kasashen sun fara tuntubar juna kan wasu sharuda da kuma shiryawa domin fara hakar man fetur na kasar Sudan ta Kudu, in ji mataimakin ministan man fetur din kasar Sudan Awad Abdul-Fatah a gaban manema labarai.
Haka kuma ya bayyana cewa, wannan zangon shawarwari ya kare cikin nasara kuma za mu fara wasu sabbin shawarwari a nan gaba, tare da nuna cewa, bangarorin biyu sun nuna fa'idar kara yalwanta dangantakarsu a wasu sauran fannoni da kuma aiwatar da ita yadda ya kamata.(Maman Ada)