Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe zai sanya hannu kan sabon kundin tsarin mulkin kasar, wanda 'yan majalisar dokokin kasar suka amince da shi a ranar Talata.
Yan majalisar sun amince da wannan sabon kundin tsarin mulki da babban rinjaye da bisa kashi biyu cikin uku da ake bukata.
Bisa 'yan majalisa 75 da suka halarci wannan zabe bisa 90 dake cikin wannan zaure, sun kada kuri'unsu domin amincewa da wannan sabon kundin tsarin mulki.
Amincewa da wannan sabon kundin tsarin mulki, na rage ikon shugaban kasa da tsawon wa'adin mulki, tare da bude hanyar gudanar da sabbin zabubuka a wannan shekara domin zaben sabuwar gwamnati da za ta maye gurbin gwamnatin hadin kan 'yan kasa da aka kafa a shekarar 2009.
Mista Mugabe na fatan ganin an shirya wadannan zabubuka kafin karshen wa'adin majalisar ta yanzu wato kafin ranar 29 ga watan Yuli, a yayin da shi kuma firayin ministan kasar Morgan Tsvangirai da jam'iyyarsa suke fatan ganin an gusa wannan rana har zuwa wani lokaci domin samun damar aiwatar da wasu sauye-sauye, ta yadda za'a iyar tabbatar da zabubuka cikin 'yanci da adalci. (Maman Ada)