in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran za ta inganta hadin gwiwa a fannoni da dama da kasar Ghana
2013-04-18 16:41:33 cri
A ranar 17 ga wata, shugaban kasar Iran Ahmadi-Nejad ya yi tattaki zuwa kasa ta karshe cikin ziyararsa a kasashen yammacin Afrika, wato kasar Ghana. A yayin taron manema labaru da aka shirya a fadar shugaban kasar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama da Ahmadi-Nejad, sun bayyana cewa, bangarorin biyu sun kafa kwamitin yin hadin gwiwa na din-din-din, kuma sun daddale yarjejeniyoyin fahimtar juna a fannonin yin hadin gwiwar kiwon lafiya, ilmi, da motsa jiki a tsakaninsu. Kazalika kuma, shugaba Nejad ya bayyana cewa, Iran za ta ba da horo game da aikin gine-ginen matatar man fetur da iskar gas ga Ghana, don inganta kwarewar kasar wajen raya sana'ar man fetur cikin dogon lokaci.

Yayin da aka tabo maganar harkokin tsaro a kasashen Afrika, da na yankin Gabas ta tsakiya, kasashen biyu sun yi Allah wadai da laifukan ta'addanci, kuma sun yi kira ga kasa da kasa, da kungiyoyin siyasa na kasashen duniya don su yi amfani da shawarwari don warware rikice-rikice. Kana kuma, bangarorin biyu sun amince da samar da taimako wajen tabbatar da zaman lafiya da karko a kasashen Mali, da Afrika ta tsakiya da kasar Kongo(kinshasa).(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China