Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Ghana ya bayar, an ce, shekarun mutanen da suka rasu na tsakanin 18 da 50 ne. shugaban hukumar 'yan sanda na garin Dunkwa Otu Larbi ya ce, wannan wurin hakar ma'adinai ya zama wani wurin hakar zinariya mai zaman kansa. Bisa shirin da aka yi, an ce, shugaban wurin hakar ma'adinai ya yanke shawarar sake maido da kasa zuwa wurin, amma mazaunan wurin sun kaurace wannan aiki, kuma wasu mazaunan kusa da wurin sun shiga wurin don hakar zinariya ba bisa doka ba, inda a daidai wannan lokaci, wannan wuri ya rushe, sannan abin da ya kawo wannan babbar hasara.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, bayan da lamarin ya auku, hukumar 'yan sanda da sauran hukumomi sun fara aikin ceto cikin gaggawa. An ce, yawan mutanen da suka rasu za a ci gaba da karuwa.(Bako)