in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Benin zai halarci taro kan zaman lafiya da tsaron Afrika a Faransa
2013-06-13 13:58:31 cri

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande ya gayyaci takwaransa na kasar Benin, Boni Yayi wajen halartar taron zaman lafiya da tsaro a Afrika da za'a shirya a birnin Paris na kasar Faransa daga ranakun 6 da 7 ga watan Disamba mai zuwa, a wani labarin da ya fito daga wasu majiyoyin diplomasiyya a birnin Cotonou na kasar Benin.

Taron na fadar Elysee kan zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afrika zai kasance muhimmin abu wajen karfafa huldar hadin kai tare da kasar Faransa, ba wai kawai da kasar Benin ba, har ma da Afrika baki daya, in ji wasikar da Francois Hollande ya aikawa mista Boni Yayi.

A cewar wannan wasika, taron zai maye gurbi bisa wani sabon salo na tarurrukan Afrika da Faransa, kana zai hada da dukkan shugabanni da gwamnatocin kasashen nahiyar Afrika. 'A cikin wannan shekarar da ta kasance cike da daukar niyyar hadin gwiwa mai muhimmanci na sojojin Afrika da na Faransa a kasar Mali, cikin jituwa tare da manufofin kungiyar tarayyar Afrika AU, ina fatan ganin an tabo muhimman batutuwan da suka shafi tsaro da zaman lafiya a nahiyar Afrika.' in ji shugaba Hollande. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China