Kwararru kimanin 40 da suka fito daga kungiyar tattalin arziki da kudi ta kasashen yammacin Afrika (UEMOA) suke tattaunawa tun ranar Laraba a Cotonou, domin shirya taro karo na 4 na ministocin kwadago da zai gudana daga ranar 16 zuwa 19 ga watan Yuli mai zuwa a hedkwatar tattalin arzikin kasar Benin.
Taron kwararru na gabannin zaman taron ministoci na da manufa yin bitar ayyukan da aka yi daga bangaren kasashen kungiyar da hukumomin ba da tallafi, aiwatar da sakamakon karshen tarurruka da kudurorin da aka cimma a tarurrukan da suka gabata, in ji ministar kananan ayyukan ba da tallafi, da samar da aikin yi ga matasa da mata, madam Sofiath Onifade.
Haka kuma ta bayyana cewa, wannan taro zai taimaka wajen nazarin hanyar dauka domin daidaita sahihancin babban jigo, ta yadda za'a gabatarwa ministocin nagartattun shawarwari.
A yayin taron shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar AU, da aka gudanar a Ouagadougou na kasar Burkina Faso a shekarar 2004, ministocin kwadagon shiyyar UEMOA suka cimma tsarin shawarwari na shekara shekara, domin bullo da hanyoyin warware matsalolin da suka fi karfin wadannan kasashe mambobi.
Manufar da ta taimaka wajen daukar matakin shirya taro karo na 4 a shekarar bana a birnin Cotonou na ministocin kwadagon kasashen UEMOA dake kunshe da Benin, Nijar, Cote d'Ivoire, Burkina Faso, Guinee Bissau, Mali, Senegal da Togo, bisa jigon shigar da matasa aikin yi, dabara da matsayin bangaren ma'aikatu masu zaman kansu.(Maman Ada)