Bankin duniya ya bullo da wata sabuwar dabara domin taimakawa kasar Benin wajen tattara da mai karfinta ga jerin muhimman ayyuka da za su taimakawa cigaba, tare da dalar Amurka kimanin miliyan 493,7 bisa wa'adin dake tashi daga shekarar 2013 zuwa shekarar 2017, in ji wata sanarwar wannan hukumar kudi ta duniya a ranar Laraba.
Wannan sabuwar dabara da bankin duniya ya gabatar ta rataya kan abkiblar ayyukan hukumomin kudin kasa da kasa a kasar Benin a tsawon shekaru biyar masu zuwa (2013-2017), musammun kan karfafa tsarin aiki na gari da karfin ma'aikatun gwamnati, bunkasa cigaba mai karko, takara da samar da ayyukan yi, kyautata cin gajiyar muhimman ayyuka ga kowa da kuma damawa tare da al'umma, a cewar wannan sanarwa.
A cewar wannan takarda, kudaden da kungiyar kasa da kasa kan bunkasuwa da sauransu suka tsai da a cikin tsarin manyan ayyuka na sabuwar dabara a cikin dangantakar bankin duniya da kasar Benin, sun shafi bangarorin taimakawa kasafin kudi, cigaban birane, muhalli, sadarwa, samar da aiki ga matasa, kiwon lafiya, samar da abincin mai gina jiki da sauransu. (Maman Ada)