Shugaban kasar Benin, Boni Yayi ya gudanar a Cotonou da bikin kadammar da mambobi bakwai wa'adi na biyar na babbar kotun kolin kasar Benin cikin aikinsu bisa wa'adin shekaru biyar masu zuwa, a wani labarin da wakilin kamfanin dillancin labaran kasar Sin na Xinhua dake wurin ya bayar.
'Jama'a maza da mata sabbin mashawarta, za ku dauki nauyi tun daga bakin wannan rana, makomar wannan babbar hukuma dake aiki domin jama'ar kasarmu, da demokaradiya da kasa mai 'yanci.' in ji shugaban kasar Benin a yayin bakin rantsar da wadannan sabbin mashawartan kotun kolin kasar Benin.
A cewar shugaba Boni Yayi, aikin da ya rataya kan kotun kolin kasa bisa dokar kasa shi ne zama wani ginshikin demokaradiya a matsayin wani makamin shari'a bisa ga tsarin mulki da makamin kiyaye harkokin 'dan adam, tare da daidaita ayyukan hukumomin gwamnati da ikon gwamnati.
A cewar kuduri mai lambar 114 na kundin tsarin mulki na 11 ga watan Disamban shekarar 1990, kotun koli na yanke hukunci kan sahihancin dokar kasa da kiyaye harkokin 'dan adam da kuma 'yancin jama'a. Haka kuma ta kasance wata hukumar daidaita ayyukan hukumomin kasa da aikin gwamnati. (Maman Ada)