Shugaban kasar Benin Boni Yayi da takwaransa na kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad sun yi kira ga kwamitin tsaro na MDD da ya shigar cikin gajeren lokaci da wani kudurin da zai taimaka wajen samar da hanyoyin tabbatar da zaman lafiya mai karko a yankin Sahel, a cewar wata sanarwar hadin gwiwa a ranar Litinin a birnin Cotonou da ta kawo karshen ziyarar shugaban kasar Iran a kasar Benin.
A yayin tattaunawar tasu, shugabannin biyu sun bayyana fargabarsu kan matsalar ta'addanci dake kamari a wasu kasashen duniya, da kuma illar wannan bala'i ga zaman rayuwar mutane baki daya, in ji wannan sanarwa.
Manyan 'yan siyasar kasashen biyu sun amince kan wajabcin daukar nagartattun matakan hadin gwiwa domin yaki yadda ya kamata da wannan annoba daga dukkan fannoni. Haka shugabannin biyu sun nuna yabo ga kokarin gamayyar kasa da kasa wajen kawar da ayyukan kungiyoyin ta'addanci a yankin Sahel.
Shugabannin biyu sun kuma mai da hankali kan wasu tashe-tashen hankali a nahiyar Afrika tare da nuna yabo ga kokarin kungiyoyin wadannan shiyyoyi da suka hada ECOWAS, CEEAC, SADC da kuma AU wajen kiyaye zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali, musammun a kasashen Mali, Guinee Bissau, Afrika ta Tsakiya da DRC-Congo. (Maman Ada)