in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Marcelline Gbeha Afouda ta zama shugabar kotun kolin shari'ar Benin
2013-06-13 13:50:39 cri

Mambobi goma sha uku na kotun kolin shari'ar kasar Benin sun zabi madam Macelline Gbeha Afouda bisa babban rinjaye a ranar Laraba a birnin Porto-Novo a matsayin shugabar wannan babbar hukuma shari'a ta kasar Benin bisa wa'adin tsawon shekaru biyar, bisa maye gurbin sheihun malami Theodore Holo wanda ba'a jima aka zabe shi shugaban kotun tsarin mulkin kasar Benin.

Marcelline Gbeha Afouda dai, an haifa ta a ranar 16 ga watan Janairun shekarar 1955, tana rike digirin karatun alkalanci mai zurfi da na digirin karatun shari'a. Madam ta taba zama tsofuwar sakatare janar kotun tsarin mulki, tsafuwar babban alkalin kasa, haka kuma ta zama mukadashin shugaban kotun tsarin mulki a cikin wa'adin aikin wannan hukuma da ya gabata.

Mai kunshe da mambobi ga shugabanta, haka kuma kotun kolin shari'ar na kunshe da 'yan majalisa 6 da shugaban majalisar dokoki da babban shugaban kotun kasa suka zaba, wannan babbar hukumar shari'a tana da nauyin gurfanar da shugaban kasa da mambobin gwamnati bisa laifin cin amanar kasa, tozarta majalisar dokoki, ko aika manyan laifuffuka a yayin da suke gudanar da aiki da makamantan haka. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China