Majalisar dokokin kasar Benin ta sanya hannu, a kwanan nan a Porto-Novo bisa rinjaye na 'yan majalisu kan sabuwar dokar kundin zabe a kasar Benin, a cewar wata majiya daga majalisar dokokin kasar.
Wannan sabuwar doka ta shafi amincewa da kundin zabe dake dauke da hadaden tsari a matsayin hanyar shari'a guda, ta zamani, kawo sauki ga tsarin zabe na yanzu a kasar Benin, in ji 'dan majalisa Karimou Chabi Sika wanda ya gabatar da wannan doka. Haka kuma ya bayyana cewa, amincewa da wannan doka zai taimaka ga kawo karshen rarrabuwar kudurorin dake tafiyar da harkokin zabe tun lokacin da kasar ta rungumi zuwan sabon sauyin demokaradiyya a cikin watan Febrairun shekarar 1990.
Kunshe da kudurori 370, wannan doka da ta shafi kundin zabe na kasar Benin za ta ba da damar kafa wani kwamitin zabe na kasa mai zaman kansa (CENA) da zai yi aiki din din din a matsayin wata kukumar shirya zabubuka mai kunshe da mambobi 5, biyu daga bangaren masu rinjaye, sannan biyu daga bangaren rukunin maras rinjaje, sannan guda da ya samu amincewa daga bangarorin biyu. (Maman Ada)