in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a wayar da kan 'yan kasuwan Najeriya kan yarjejeniyar cinikayya karkashin ECOWAS
2013-06-13 10:46:20 cri

Darektan cinikayya David Adejuwon shi ne ya wakilci ministan masanan'antu da cinikayya, inda ya ce, ganawar da suka yi da 'yan kasar Ghana ya yi nasara domin an cimma yin adalci dangane da daukacin batutuwan da suka shafi yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashen ECOWAS, kamar a 'yancin fuskar kasuwanci, zirga-zirgar jama'a da kuma zama a waje.

Ya ce, yadda ake harkar cinikayya tsakanin kasashe na kara kawo bunkasar kasuwanni a kan iyakoki kuma hanyar Lagos-Seme-Abidjan na samun cunkoso, don haka ya dace a samar da wasu sabbin hanyoyin da za su haifar da samun bayanai masu gamsarwa kan yarjejeniyar cinikayya na ECOWAS din, cikin sauki.

Taron ya bayyana cewa, Najeriya ta gano wasu cin zarafi da wasu kasashen kan yi a karkashin shirin na ETL, inda ake barin kayayyaki da ba na yankin ba shiga rukunin na yankin.

An jadadda cewa, gwamnatoci na dauke da nauyin kare tattalin arzikinsu don kaucema matsala tare da kira ga hukumar ECOWAS da ta dan yi sassauci wajen aiwatar da yarjejeniyar cinikayya ta ETL domin kasashe su samu kare masana'antunsu da kuma yin daidaito a cinikayya. (Lami)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China