Kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWAS ta sanya hannu aljihu domin tallafawa noman kofi a kasashen Sierra Leone da Laberia bisa kudin Amurka miliyan 75, a cewar wani jami'i a ranar Litinin.
Wannan shiri na tsawon shekaru goma sha biyar, zai fara aiki a shekara mai zuwa, kuma zai mai da hankali wajen sake ba da azama kan noman kofi da ya rasa tagomashi a lokacin yake-yake a cikin wadannan kasashe biyu.
Bayan wani zaman taron kwararru na kwanaki uku domin fadakar da masu noman kofi na Sierra Leone da Laberia, babban darektan kasuwancin kayayyaki na kasar Laberia (LPMC), mista Nyan Matein ya bayyana cewa, wannan shiri zai kuma mai da hankali wajen bunkasa kwarewar manoman kofi na kasashen biyu yadda ya kamata. (Maman Ada)