Kungiyar ECOWAS ta dauki niyyar kara yawan jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda zuwa kasar Guinee-Bissau domin tabbatar da tsaro a lokacin zabubukan da za'a gudanar a cikin wannan shekara, a cewar wata sanarwar da ta fito a ranar Talata a Bissau bayan wani zaman taron kwamitin tsaron wannan kungiya ta yammacin Afrika.
Halin da ake ciki yanzu a kasar Guinee-Bissau, na bukatar tura karin 'yan sanda da sojoji, in ji shugaban rundunar sojojin kasar Cote d'Ivoire, mista Soumaila Bakayoko kuma shugaban kwamitin tsaron ECOWAS a yayin da yake hira da manema labarai, kan wannan mataki na kara yawa da karfafa karfin 'yan sanda.
Taron da ya tattara shugabannnin rundunar sojojin kasashen Senegal, Cote d'Ivoire, Najeriya da Burkina-faso, kasashen da suka tura wata tawagar dake kunshe da sojoji da 'yan sanda 680, ya bukaci gaggauta gyare-gyare a bangaren kiyaye tsaron kasar Guinee-Bissau.
Wannan kasa za ta samu zaman lafiya mai karko idan aka aiwaitar da wadannan gyare-gyare, in ji janar Bakayoko. (Maman Ada)