Ministan lura da harkokin hadin gwiwar kasashen Afirka a Cote d'Ivoir Ali Coulibaly, ya bayyana aniyar kungiyar ECOWAS, don gane da gudanar da wani taro na musamman, da nufin nazartar halin tsaron kasar Mali a ranar Laraba 16 ga wata. Taron wanda aka tsara gudanarwa a birnin Abidjan, ana sa ran zai samu halartar shuwagabannin kasashe mambobin kungiyar ta ECOWAS. Bugu da kari Coulibaly ya tabbatar da fara hallarar sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar a Mali ranar Lahadin da ta gabata.
Shugaba Alassane Outtara na Cote d'Ivoir, da ke matsayin jagoran kungiyar na karba-karba ya jaddada fara aiwatar da kudurin MDD, na girke tawagar sojoji 3,000 a kasar ta Mali, a matsayin gudunmawar kasashen Afirka, ga yakin da Malin ke yi da kungiyoyin 'yan tawaye, musamman ma a yankunan arewacin kasar, inda tuni sojojin Nigeria da na Faransa suka sauka a Bamako, domin fara aiwatar da ayyukan tallafi ga kasar ta Mali, kamar dai yadda aka tsara.(Saminu)