in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya rage saurin bunkasar tattalin arzikin duniya zuwa 2.2 a 2013
2013-06-13 10:31:49 cri

A ranar Laraban nan babban bankin duniya ya rage saurin bunkasar tattalin arzikin duniya zuwa kashi 2.2 cikin dari a wannan shekara, wato ke nan an samu raguwar 0.2 idan aka kwatanta da hasashen da aka yi a watan Janairu.

An samu dan sassaucin barazana daga kasashe masu bunkasar tattalin arziki a duniya, kuma ana dan samun ci gaba duk da yanayin da ake ciki a kasashen kungiyar Euro. Babban bankin dake da hedkwata a Washington ya bayyana cikin rahoton na baya bayan nan kan makomar bunkasar tattalin arzikin duniya (GEP) cewa, bunkasa a kasashe masu tasowa ba zai yi yawa ba saboda 'yan matsaloli da ake fuskanta a kasashe masu matsakaicin albashi.

Ana sa rai cewa, amfani da ake samu daga kayayyaki na cikin gida (GDP) zai karu zuwa 2.2, kana yana iya ci gaba zuwa 3.0, da kuma 3.3 a shekarun 2014 da 2015 daki daki, in ji rahoton.

Haka zalika, ana sa rai cewa, GDP na kasashe masu tasowa zai bunkasa zuwa 5.1 a wannan shekara wato an samu raguwar 0.4 bisa hasashen da bankin ya bayar a watan Janairu, sannan zai haura zuwa 5.6 da kuma 5.7 a shekarun 2014 da 2015 daki daki.

Bunkasa a kasashen Brazil, Indiya, Rasha, Afirka ta Kudu da Turkiya sun samu dan koma baya saboda wasu 'yan matsaloli. Duk da cewa, an samu sassauci daga waje a fuskar shigo da kayayyaki, ana ganin cewa, yana da wuya a samu ci gaba kamar yadda aka samu kafin a shiga matsalar tattalin arzikin duniya, sai an yi gyare-gyare. A kasar Sin, an samu koma bayan bunkasa yayin da mahukunta ke kokarin yiwa tattalin arzikin daidaito. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China