Mr. Zoellick ya ce shugabannin kasashen duniya masu karfin tattalin arziki su na bukatar sake daidaita tunanin su akan batun da ya shafi tattalin arzikin su.
Yanzu haka dai shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki suna gudanar da wani taro wanda batun manufofin da suka shafi hada hadar kudade ya kasance babban batun da aka fi tattaunawa akai.
Shugaban bankin duniyar ya cigaba da cewa yanzu abun da ake bukata shi ne yin gyare gyare da za su haifar da samuwar guraben aiyukan yi, samar da horo, don samun daidato mai dorewa ta fuskar tattalin arziki, inda ya ce abun dake faruwa a kasar Sin yana da mahimmanci a kasashe irin su Japan, Amurka da yankin turai.
An dai tsara cewa Mr Robert Zoellick zai kawo ziyara kasar Sin a tsakanin ranar 1zuwa ta 5 ga wannan watan domin tattaunawa akan irin kalubalen da kasar ta fuskanta wajen daidaita harkokin tattalin arzikinta.
Wannan ziyara da zai kawo ita ce ta biyar tun bayan kasancewarsa shugaban bankin duniyar.
A lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaru na kasar Sin ranar talatar nan data gabata a jajiberin ziyarar sa, Mr Zoellick ya bukaci sauran kasashe da su yi koyi da salon dabarun da kasar Sin ta yi amfani da su wajen kare masu karamin samu daga shiga halin kaka-nikayi. (BAGWAI)