Mr. Abdoulaye Makhtar Diop ya kuma jadadda cewa, sabo da a halin yanzu, karancin abinci, tabarbarewar yanayin tsaro, da kuma rikicin siyasa da kasar Mali ke fama da su, sun riga sun kawo illa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar, dalilin haka, kasar take bukatun taimakon gamayyar kasa da kasa sosai. (Maryam)