in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harkar zuba jarin kasashe masu tasowa a duniya zai ninku nan da shekarar 2030, in ji bankin duniya
2013-05-17 10:49:43 cri

Babban bankin duniya yayi hasashe ranar Alhamis cewa, kasashe masu tasowa za su rubanya jari da suke zubawa zuwa kashi 60 cikin dari na iya yawan adadin jarin duniya, nan da shekarar 2030.

Wani rahoton babban bankin na hangen nesan bunkasa a duniya baki daya ya yi hasashen cewa, a wannan lokaci, rabin adadin yawan kudaden zuba jari na duniya, wanda ya kai dalar Amurka triliyon 158 a shekarar 2010, za su kasance ne a kasashe masu tasowa, inda hakan ya sha banban da yanayin da ake ciki yanzu, inda adadin bai ma kai kashi daya cikin uku ba.

Rahoton ya ci gaba da nuna cewa, nan da shekarar 2030, kasar Sin za ta zamo mai zuba jari a duniya da yawansu ya kai kashi 30 cikin dari, sannan kasashen Brazil, Indiya da Rasha baki daya nasu zai kai kashi 13 cikin dari.

Wannan sauyi na karuwar yawan zuba jari yana da alaka ne da haurawar riba da ake samu daga albarkatu a kasashe masu tasowa.

A halin yanzu, kashi 70 cikin dari na yawan ribar da ake samu daga albarkatu a fadin duniya, ana samu ne a kasashe da suka bunkasa, to amma adadin zai yi kasa zuwa kashi 50 cikin dari a shekarar 2030.

A fadar rahoton, nan da shekarar 2030, kasashe masu tasowa su ne za su zamo kan gaba a fuskar bunkasa a duniya, inda kasonsu zai kai kashi 87 cikin dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2015, wanda zai kai kashi 73 cikin dari, kana su ne za su zamo kan gaba a harkar cinikayya a duniya, wanda yawan shi zai kai kashi 50 cikin dari a lokacin.

To amma Maurizio Bussolo wanda shi ne shugaban masu hada wannan rahoto ya yi nuni da cewa, duk da cewa, dukiya za ta samu yaduwa a duniya, ba wai ana nufin cewar, kowane mutum zai ci moriyar hakan ba ne a cikin kasashe.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China