Bankin duniya ya dauki niyyar rubanya taimakonsa ga kasar Nijar ta hanyar zuba jari a wannan kasa, daga dalar Amurka miliyan 400 zuwa fiye da dalar Amurka miliyan 800, in ji darektan ayyukan bankin duniya mista Ousmane Diagana bayan wata ganawarsa tare da shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou.
Bankin duniya na gudanar da ayyuka da dama a kasar Nijar kuma wannan taimako zai shafi fannonin ilmi, kiwon lafiya, jama'a, noma, kiwo, cigaban yankuna da na karkara da ma'aikatun kudi na gwamnati, in ji mista Diagana.
Haka kuma jami'in ya gabatar da ta'aziyar bankin duniya bayan hare-haren ta'addanci na biranen Agadez da Arlit da kuma gidan kurkukun birnin Yamai.
An yi gasanar a gaban ministan harkar kasa, dake kula da fasalin kasa Amadou Boubacar Cisse da kuma wakilin bankin duniya dake kasar Nijar Ernest Koffi. (Maman Ada)