Bankin duniya ya gabatar da wani rahoto game da makomar tattalin arziki a nahiyar Afirka a wannan rana, inda ya bayyana cewa, kashi daya cikin kashi hudu na kasashen yankin Afirka dake kudu da hamadar Sahara sun samu karuwar tattalin arziki fiye da kashi 7 cikin kashi dari, inda wasu daga cikinsu suka kasance kasashe mafi samun bunkasuwa a fadin duniya.
A sakamakon farfadowar tattalin arzikin duniya da karuwar bukatun cikin gida, tattalin arzikin kasashen Afirka zai ci gaba da samun karuwa.
Hakazalika, bankin duniya ya nuna cewa, a shekaru fiye da 10 da suka wuce, bunkasuwar tattalin arziki na taimakawa kasashen Afirka wajen kawar da talauci, amma matsalolin rashin daidaici da kara dogora da albarkatun kasa yayin da ake raya tattalin arziki sun kawo cikas ga kawar da talauci a kasashen Afirka ta hanyar yin amfani da bunkasuwar tattalin arzikinsu. (Zainab)