in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya sabunta takunkumin makamai a Kwadibwa na karin shekara daya
2013-04-26 09:54:47 cri

A ranar Alhamis, kwamitin tsaron MDD ya sake sabunta takunkumin a kasar Kwadibwa na karin shekara guda, har ma da takunkumin kan makamai da kuma shiga da dutse mai daraja na diamond daga kasar ta Afirka, wacce ke ci gaba da fama da matsalar tsaro.

Kwamitin tsaron mai mambobi 15 ya bayyana cikin wani kuduri da aka amince cewa, daga nan zuwa ran 30 ga watan Aprilu shekarar 2014, dukkan kasashen za su dau matakai na hana sayarwa ko kuma shiga da makamai kai tsaye ko kuma ta wata hanya zuwa cikin kasar Kwadibwa.

A fadin kudurin, kwamitin tsaron har wa yau ya tsai da shawarar yin kari na tsawon shekara daya, na matakan kudade da na sufuri da kuma matakan hana kasashe sayen duwatsun diamond daga kasar Kwadibwa, bisa takunkumi na baya da aka kakaba ma kasar.

Sabunta wannan kuduri ya zo ne kwana daya bayan gwabzawa tsakanin jami'an 'yan sanda da masu zanga-zanga a kasar bayan sanarwar da aka yi a talbijin din kasar na sakamakon zaben kasar.

Yanayin da ake ciki na rashin tabbas, barazana ce ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa a yankin, in ji kwamitin.

To amma, wadannan kudurori ba za su shafi samar da kayayyakin da suka shafi aikin kiyaye zaman lafiya na MDD a kasar ba, ko kuma wadanda za'a kawo don tallafawa bil Adama.

Tun cikin watan Nuwamban 2004, kwamitin tsaron na MDD ya kakabawa kasar kwadibwa takunkumi dangane da makamai.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China