in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani dan kasuwa daga kasar Indiya, ya sayi wata kungiyar kwallon kwando ta kasar Amurka
2013-06-13 09:34:19 cri
A kwanakin baya, hukumar wasan kwallon kwando ta kasar Amurka ta sanar da cewa, majalisar hukumar ta amince da sayar da kungiyar Sacramento Kings, ga shugaban kamfanin Tibco Software na kasar Indiya Vivek Y. Ranadive, kan kudi da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 347.

Tun dai daga shekarar 1999, Iyalin wani dan kasuwa mai suna Maloof suka mallaki kungiyar ta Sacramento Kings. Amma a farkon shekarar bana, babban jami'in kamfanin Microsoft Steve Ballmer, ya taba bayyana ra'ayinsa na sayen wannan kungiya, sai dai ya nuna bukatar kaura da wannan kungiya zuwa birnin Seattle, don haka babban taron kamfaninsa ya ki amincewa da shirin.

Ranadive dan shekaru 55 daga kasar Indiya, wanda ya kafa wani kamfani da darajarsa jarinsa ta kai fiye da dala miliyan 100, kwararren Injiniya, kuma marubucin littattafai, Ranadive ya wallafa litattafan hada-hadar kudi da dama. Sharadinsa na sayen kungiyar Sacramento Kings shi ne, a kara gina sabon filin wasa na kwallon kwandon, wanda zai iya daukar mutane 18,500.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China