A: Domin Oklahoma Thunder ta fi samun nasara a gasar zagayen farko ta NBA a wannan karo, sabo da haka, za a yi gasa guda 4 a cikin gasa guda 7 na wasar karshe a Oklahoma a wannan karo. Za a yi wasa guda 2 a Oklahoma, daga baya yi wasanni 3 a Miami, a karshe yi wasanni 2 a Oklahoma.
Bayan da aka fitar da kungiyoyi biyu da suka shiga gasar karshe ta NBA a wannan karo, ESPN ta yi hasashe ba tare da bata lokaci ba. A tawagar masana guda 14, guda 9 sun zabi Oklahoma Thunder da za ta yi nasara.
Amma dukkan masanan sun yi tsammani cewa, wasar dake tsakanin kungiyoyin biyu za ta zama wasa mai sha'awa sosai. Yawancinsu sun ce, za a yi dukkan wasanni 7 a wannan karo.
Hakazalika, masu sha'awar wasan kwallon kwando sun jefa kuri'u a shafin internet na ESPN. Ya zuwa yanzu, mutane 53 185 su ka jefa kuri'u, kashi 67 cikin dari sun na sa ran cewa, Oklahoma Thunder za ta zama zakara. Kashi 33 cikin dari kawai su ka zabi Miami Heat.(Zainab)