in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Miami Heat ta yi rinjaye a zagayen wasar karshe ta NBA a wannan karo
2012-06-20 16:13:40 cri
A ranar 18 ga wannan wata, an kammala wasan 3 na zagayen gasar karshe ta NBA a jihar Miami. A karshe, kungiyar Miami Heat ta lashe kungiyar Oklahoma Thunder, da cin 91 da 85. wadda ta yi rinjaye a zagayen wasar karshe ta NBA a wannan karo.

A wannan wasa, muhimman 'yan wasan kungiyar Miami Heat da ake kiransu Big 3 wato (shika-shikai uku) sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasara a wasar. LeBron James ya samu maki 29, Dwyane Wade ya samu maki 25, shi kuma Chris Bosh ya samu maki 10.

Bayan kwana guda na hutu, kungiyoyin biyu za su ci gaba da yin wasa a jihar Miami a ranar 20 ga wannan wata.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China