Za a gudanar da gasanni biyu a tsakanin kungiyoyin biyu a ranar 11 ga watan Oktoba a birnin Beijing da kuma a ranar 14 ga watan Oktoba a birnin Shanghai.
Wannan ne karo na 6 da aka gudanar da wasan share fagen gasar NBA a kasar Sin, kana wannan ne karo na farko da kungiyar da ta zama zakara a gasar karon da ya gabata ta kai ziyara kasar Sin don yin gasa.
Kungiyoyin biyu suna da 'yan wasa da suka kware a duniya da dama. A kungiyar Miami Heat, akwai LeBron James, Dwyane Wade, Chris Bosh da kuma Ray Allen. Kana a kungiyar Los Angeles Clippers, akwai 'yan wasa irinsu Blake Griffin, Chris Paul, Chauncey Billups da kuma Lamar Odom.
Wasan share fagen na gasar NBA a kasar Sin yana daya daga cikin wasannin share fage na gasar NBA da aka gudanar a kasashen waje a shekarar bana. A watan Oktoba na bana, kungiyoyi 8 na NBA za su halarci gasanni 8 a wajen Amurka. (Zainab)