in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan wasan NBA 7 sun halarci wani aikin sa kai mai taken "Basketball without Borders" da aka gudanar a nahiyar Afirka
2012-09-05 12:10:51 cri
An ce, 'Yan wasan NBA 7 sun halarci wani aikin sa kai mai taken "Basketball without Borders" da aka gudanar a nahiyar Afirka a bana. A cikinsu, guda 4 'yan wasa na kungiyar Oklahoma City Thunder. Su ne Nick Collison, Serge Ibaka, Thabo Sefolosha, da kuma Cole Aldrich.

Aldrich ya ce, ya zo nahiyar Afirka ne ba ma don canja zaman rayuwar jama'a a nan kawai ba, hatta ma don canja zaman rayuwar kansa, wato zai kalli zaman rayuwar sauran mutane. Wato tilas ne zai ci gaba da gudanar da wannan aikin sa kai, wato taimakawa mutane ta hanyar yin amfani da sunan wasan kwallon kwando.

Shi kuma Ibaka ya koma garinsa wato birnin Brazzaville dake kasar Congo, inda ya koyar da yaran dake wurin ilmin rayuwa da na maganin cutar kanjamau.

Iyayen Ibaka 'yan kasar Congo Brazzaville ne, kana dukkansu 'yan wasan kwallon kwando ne. Sabo da haka, Ibaka yana kokarin yada wasan kwallon kwando a nahiyar Afirka. A halin yanzu, Ibaka yana daya daga cikin fitattun 'yan wasan NBA dake da kwarewa a fannin tsaron gida.

Mahaifin Sefolosha dan kasar Afirka ta kudu ne, shi da Ibaka da kuma Collison sun taba halartar aikin sa kai na "Basketball without Borders", kuma wannan ne karo na farko da Cole Aldrich ya halarci wannan aiki.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China