A wannan rana kuma, kungiyar Miami Heat ta lashe ta Indiana Pacers da ci 95 da 86, wadda ta samu maki daya a wasan kusa da na karshe ta yankin gabashin Amurka ta NBA.
Kafin wannan wasa, dan wasa na kungiyar Miami Heat, mai sunan Le Bron Raymone James, ya samu lambar yabo ta MVP a wannan karo, wannan ne karo na uku da James yake samun wannan lambar yabo. Amma James ya ce, yana son yin amfani da wadannan lambobi yabo guda 3 don musayar zobe guda na zakara na wasan kwallon kwando na NBA.
Ban da wannan kuma, a ranar 13 ga wannan wata, a wasa na daban na kusa da na karshe a yankin gabashin Amurka ta NBA, kungiyar Boston Celtics ta lashe da ta Philadelphia 76ers ci 92 da 91, wadda ta samu maki daya a wasan kusa da na karshe ta yankin.(Zainab)