Wata takardar sanarwa da ta kai ga kamfanin dillancin labarai na kasar Sin (Xinhua) ta ce, John Idoko, babban daraktan hukumar shawo kan yaduwar kwayoyin cutar HIV da kan haddasa kanjamau ta kasa a Najeriya (NACA), shi ne ya yi kiran ranar Litinin din makon nan a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, yayin taro a karo na 16 na kasa da kasa da ake yi kan kwayoyin cutar HIV da sauran cutuka da a kan kamu da su ta hanyar jima'i a Afirka.
Idoko ya ce, yanayin samar da inshorar kiwon lafiya a Afirka ba abu ne mai karfafa gwiwa ba, don haka ya yi kira ga shugabanni da su rungumi akidar tallafawa, lamarin da zai ba su damar samar da kudi sosai don samun inshorar.
Daraktan NACA din ya ce, shirin samar da inshorar kiwon lafiya yana aiki sosai a Najeriya, kana a watan Janairu za'a yi wani taron masu ruwa da tsaki, inda za'a yi la'akari da hanyoyi na hakika wajen samar da kudi.
Ya kuma bayyana bukatar sa hannun gwamnatoci a matakan kananan hukumomi da jihohi wajen samar da kudi a yunkurin fatattakar cutar ta kanjamau.
John Idoko ya ce, akwai bukatar gwamnatoci su cika alkawuransu ta hanyar yin aiki don samun ingancin shirin da aka tsara kan Afirka. (Garba)