in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron BRICS zai kawo karin alheri ga kasashe mambobi da ma nahiyar Afirka
2013-03-26 14:16:14 cri

Tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria Alhaji Atiku Abukakar, ya ce, taron kasashe mambobin kungiyar BRICS, karo na 5 da za a gudanar a Afirka ta Kudu ranar 26 da 27 ga wata, zai habaka ci gaban kasashe mambobin kungiyar, da ma daukacin kasashen dake nahiyar Afirka.

Atiku wanda ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua hakan, ya kara da cewa, taron zai samar da dimbin hanyoyin da za a iya mora, musamman ma a fannin kasuwanci, cinikayya da harkokin zuba jari. Ya ce, a ganinsa, lokaci ya yi da kasashen nahiyar ta Afirka za su rungumi wannan dama da kungiyar ta BRICS za ta samar, duba da cewa, tsahon lokaci, kasashen Turai ne ke mamaye huldodin da Afirkan ke yi da ragowar sassan duniya.

Bugu da kari, tsohon shugaban kasar na ganin ita ma wannan kungiya za ta kwashi riba mai tarin yawa daga kudaden cinikayyar waje, duba da irin damammaki da nahiyar Afirka ka iya samarwa ta fuskar cinikayya, duk kuwa da kasancewarta nahiya mai tasowa a yanzu. Atiku na fatan kungiyar ta BRICS za ta dada fadada a nan gaba, ta yadda Nigeria za ta shiga a dama da ita wajen ciyar da duniya gaba.

Don gane da kafuwar bankin kungiyar kuwa, Atiku ya ce, hakan wani ginshiki ne na kafa wani jigo irinsa na farko, da zai bunkasa ci gaban wannan yanki da ma duniya baki daya. Daga nan sai ya bayyana fatan hadin gwiwa tsakanin BRICS da ragowar kasashen Afirka, wajen cimma burin da aka sanya gaba.

Kungiyar BRICS dai ta kunshi kasashe biyar masu saurin bunkasuwar tattalin arziki, da suka hada da Brazil, da Russia, da India, da Sin, da kuma Afirka ta Kudu. An kuma kafa ta ne da zummar bunkasa ci gaban wadannan kasashe ta fuskar masana'antu da habakar arziki.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China