Kamfanin dillancin labarai na kasar Sudan SUNA ya ba da rahoto cewa, wata tawaga daga kasar Sudan ta Kudu ta isa Khartoum, babban birnin kasar Sudan ranar Laraba da nufin kammala shirin maido da fitar da mai zuwa waje ta cikin yankin arewa daga yankin kudu.
Tawagar wacce ta taho daga ma'aikatar man fetur ta kasar Sudan ta Kudu za ta tattauna da takwarorinta na kasar Sudan dangane da aiwatar da yarjejeniya a wannan fuska, in ji rahoton.
A kwanan nan ne majalisar dokokin kasar Sudan ta sanar da cewa, za ta fara fitar da mai zuwa waje ta bututu mallakar kasar Sudan daga 31 ga watan Maris kamar yadda yake kunshe a yarjejeniya da aka kulla tsakanin Khartoum da Juba a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Bangarorin biyu suna rikici da juna dangane da batun kudi da Sudan ta dage cewa, Sudan ta Kudu ta biya saboda amfani da na'urorinta wajen fitar da man.
A cikin watan Janairun 2012, Sudan ta Kudu ta dakatar da tura mai ta cikin Sudan saboda kasar tana diban man wanda take cewa, ta diba ne a madadin kudin da za'a biya ta na amfani da na'urorinta.(Lami)