in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya na shirin shirya taron kasa da kasa game da batun Siriya
2013-05-15 16:52:55 cri
Kwanan baya, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov da sakataren harkokin wajen Amurka John Forbes Kerry sun daddale yarjejeniya game da batun Siriya, inda bangarorin biyu suka amince da shirya wani taron kasa da kasa game da batun kasar,don ingiza yunkurin warware rikicin Siriya ta hanyar da ta dace.

A ranar 14 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius, ya bayyana cewa, shirya wani taron kasa da kasa da zai samu halartar wakilan gwamnatin Siriya, da bangaren 'yan adawa na da wuya ainun, amma, duk da hakan, Faransa ta nuna goyon baya game da batun. Ya bayyana cewa, kasashen da abin ya shafa na kokarin shirya taron a karshen watan Mayun bana.

A ranar 14 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Siriya ya bayar da labari cewa, kwanan baya, ministan yada labaru na Siriya Omran Al-Zoubi ya bayyana cewa, kafin Siriya ta yanke shawara ko ta shiga taron, gwamnatin tana bukatar karin bayani game da taron, sabo da ba za ta shiga ko wane irin aiki ko taro da zai lahanta mulkin kai na kasar.

A ranar 14 ga wata, a birnin Beirut, manzon musamman na shugaban kasar Amurka kuma mai shiga tsakani game da batun Gabas ta tsakiya da arewacin kasashen Afrika da ke yin ziyara a Lebanon Phillip ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa a yankin Gabas ta tsakiya, da kada su dauki matakan da za su tsananta rikicin kasar ta Siriya.

Ban da wannan kuma, a ranar 14 ga wata, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu su ma sun yi shawarwari, inda bangarorin biyu suka tabo batun kasar ta Siriya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China