in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai sauran rina kan batun 'yan kungiyar Al-Shabaab, in ji shugaban Somaliya
2013-05-27 09:40:42 cri

Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheik Mohammed ya bayyana ranar Lahadi cewa, duk da cewa an tarwatsa 'yan kungiyar Al-Shabaab, akwai sauran rina a gaba domin kuwa har yanzu kungiyar babbar barazana ce ga kasar Somaliya, yankin, da ma duniya baki daya.

Yayin babban taron kungiyar AU wanda ya zo daidai da cika shekaru hamsin da kafa kungiyar tarayyar hadin kan kasashen Afirka dake kankama a birnin Addis Ababa, kasar Habasha, shugaban na Somaliya ya bayyana wa 'yan jarida cewa, gwamnatin dake mulki a kasar yanzu ta cimma nasarori da dama tun daga lokaci da ta hau karagar mulki watanni takwas da suka gabata.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin kasar ta Somaliya na fama da wasu kalubale da suka shafi cibiyoyin gwamnati, dakarun tsaro da tsarin shari'a da dai sauransu.

Ya ce, hadin kan kasar shi ne babban abu da wannan gwamnati ta sa gaba, kuma za ta yi hakan ne ta hanyar zaman lafiya da tattaunawa.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China