in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya da Somaliya za su yi aiki tare domin magance barazanar kungiyar Al-Shabaab
2013-06-06 10:48:35 cri

Shugabannin kasashen Kenya da Somaliya a jiya Laraba suka sanar da cewa, sun umurci rundunar tsaron kasashensu gaba daya da su yi aiki kafada da kafada domin kawar da barazanar kungiyar nan ta Al-Shabaab, wadda ake zargi da aiwatar da dimbin hare-hare da kisan jama'a a kasashen biyu.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta wanda ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar sakamakon ganawarsa da Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud wanda ke ziyara a Nyeri dake tsakiyar kasar ta Kenya, ya ce, sun riga sun bukaci goyon bayan hukumar IGAD, ofishin kula da 'yan gudun hijira na MDD da sauran kungiyoyi masu alaka da irin ayyukan agaji na duniya da su tabbatar da samun nasarar wannan kuduri.

Kasashen biyu dake makwabtaka da juna suna zargin 'ya'yan kungiyar da hannu a cikin yawan hare-haren da ake kaiwa, musamman a arewacin kasar Kenya da kuma kasar ta Somaliya dake kusurwar Afrika, abin da ya hada da yin garkuwa da baki.

Mahukuntan kasar Kenya sun ce, yin garkuwa da ake yi da baki yana kawowa babban barazana ga aikin yawon shakatawa wanda shi ne babban aikin gwamnati dake kawo kudaden shiga kuma fannin da shi ne babbar hanyar tattalin arzikin yankin.

Kungiyar Al-Shabaab dai ta dade tana fada domin son hambarar da gwamnatin Somaliya tun shekarar ta 2008. Kuma ita wannan kungiya ana ganin tana da alaka da kungiyar Al-Qaida, kungiyar da kasar Amurka ta yi ma sunan babbar kungiyar yan ta'adda ta duniya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China