in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu tada kayar baya sun sake shirya kai hari a Chadi, a cewar shugaban Niger
2013-05-28 10:20:22 cri

Shugaban jamhuriyar Niger Mahamadou Issoufou ya fada a ranar Litinin yayin wata hira da gidan talabijin na kasar Faransa mai suna 'France 24' cewa, 'yan ta'addan da suka kai tagwayen hare-hare a Niger suna shirya kai wani harin a kasar chadi.

Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci garin Agadez dake tsakiyar kasar, inda aka kai hari kan barikin soja a ranar Alhamis din da ta gabata, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar sojoji 24, inda ya ce, ko da ya ke ba a kai harin na Chadi ba, amma an shirye su ne tare da wadanda aka kai a kasar ta Niger.

Kwamandan kungiyar MUJAO mai kaifin kishin Islama Mokhtar Belmokhtar cikin wata sanarwa, ya ce, kungiyar ce ta kai wadannan hare-hare, a matsayin ramuwar gayya bisa matakin da Niger din ta dauka na tura sojojinta don mara baya ga shirin sojojin kasar Faransa na daukar matakan soja kan masu tada kayar baya da ke da alaka da kungiyar al-Qaeda a kasar Mali.

Shugaban na Niger ya sha yin gargadin cewa, rikicin Mali ya haifar da matsalar cikin gida a kasarsa, inda ya ce, 'yan kunar bakin waken da suka kai tagwayen hare-haren ranar 23 ga watan Mayu a garuruwan Arlit da Agadez, sun fito ne daga kudancin kasar Libya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China