Babban sakatare na MDD, Ban Ki-moon ya yi allawadai da babbar murya a ranar Alhamis, bayan abkuwar wasu hare-haren kunar bakin wake a wannan rana a arewacin kasar Nijar.
Babban jami'in MDD ya sake jaddada goyon bayan kungiyarsa ga kokarin da gwamnatin Nijar take da ma sauran kasashe dake yankin Sahel domin yaki da annobar ta'addanci da kisan kan kasa da kasa, tare da taimakon kungiyar tarayyar Afrika AU, kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS da kungiyar kasashen dake tsakiyar Afrika, a cewar wata sanarwa da kakakin Ban Ki-moon ya karanta.
Gaba daya mutane 25 suka mutu, a ciki, suka hada da sojojin kasar 20 da 'yan ta'adda 5, a lokacin wadannan hare-hare na ranar Alhamis da suka abku a wani sansanin soja na jihar Agadez dake arewacin kasar da kuma kamfanin hakar ma'adinai na Somair, wani reshen kamfanin Areva na kasar Faransa dake birnin Arlit a arewacin kasar, in ji ministan tsaron kasar Nijar Karidjo Mahamadou.
Haka kuma mista Ban ya jaddada muhimmancin gamayyar kasa da kasa wajen cigaba da karfafa taimakonta, ta yadda za'a kokarin murkushe barazanar ta'addanci domin tabbatar da zaman lafiya mai karko a wannan shiyya, da ma duniya baki daya. (Maman Ada)