in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hare-haren kunar bakin wake biyu sun halaka mutane 25 a arewacin Nijar
2013-05-24 10:36:04 cri

A kalla mutane 25 da suka hada da sojoji 20 da 'yan kunar bakin wake 5 suka mutu a wasu tagwayen hare-haren da aka kai a ranar Alhamis a wani barikin soja a jihar Agadez dake arewacin kasar da Somair, wani reshen gungun kamfanin Areva na kasar Faransa dake birnin Arlit a arewacin kasar, in ji ministan tsaron kasar Nijar Karidjo Mahamadou. Haka kuma ya ce, mutane 30 suka ji rauni, daga cikinsu akwai sojoji 16 da fararen hula 14.

A cewar wata sanarwa ta ma'aikatar tsaron kasar Nijar, a wannan rana ta Alhamis da misalin karfe biyar da rabi na safe, gungu biyu na wasu mutane dauke da makamai da nakiyoyi a cikin motoci kirar Toyota, sun kai hari kan wani sansanin soja na Agadez da kamfanin hakar ma'adinai na Somair bisa aikata munanan hare-hare.

'Wadannan hare-haren ta'adanci da 'yan kunar bakin wake suka kai ya ci karo da sojojin gwamnatin kasarmu, kuma duk asarar abokansu sun ja daga tare da dakile da wadannan 'yan kunar bakin wake, ko da wasu daga cikinsu sun tada nakiyoyin dake jikinsu.' in ji wannan sanarwa. A dunkule sojoji 20 suka mutu yayin da 16 suka ji rauni, uku suka mutu daga cikin maharen a jihar Agadez, kana a birnin Arlit, fararen hula 14 suka ji rauni a yayin da biyu daga cikin maharen suka mutu.

Tuni dai kungiyar 'yan kishin Islama da Jihadi a yammacin Afrika (MUJAO), ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare, wato wani gungun kishin Islama da Jihadi na kasar Mali, a cewar Karidjo Mahamadou.

Yanzu kura ta kwanta, kuma ana cigaba da farautar wasu daga cikin wadannan mahara, kuma za'a cigaba da sanar da al'umma kan halin da ake ciki, in ji minista Karidjo.

Tuni dai al'umma Nijar da gwamnatin kasar suka shiga zaman makoki na tsawon kwanaki uku tun daga ranar da wadannan hare-hare suka abku. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China