Faraministan kasar Cote d'Ivoire, Daniel Kablan Duncan ya kaddamar da ayyukan ginin wata tashar samar da ruwa a ranar Talata domin kyautata da warware matsalar ruwan sha da birnin Abidjan, hedkwatar tattalin arzikin kasar yake fuskanta. Ginin mai daukar cubic mita 5000 na cikin da'irar Anyama dake yankin arewacin birnin Abidjan zai taimaka wajen warware matsalar karancin ruwan sha masu tsabta da kashi 30 cikin 100 a birnin Abidjan.
Mista Duncan ya bayyana cewa, akwai wani shirin gaggawa na kudin Sefa biliyan 48 kimanin dalar Amurka miliyan 95 da aka kebe domin warware wannan matsala a birnin Abidjan. (Maman Ada)