A yanzu haka shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad yana wata ziyara a kasashen yammacin Afirka guda uku, ciki har da Benin, Nijar da kuma Ghana.
Ahmadinejad ya bar Iran ya isa kasar Benin ne da maraicen ranar Lahadin da ya gabata, wadda ta kasance kasa ta farko a ziyararsa a wannan karo. Kafin ziyararsa a wannan karo, kafafen watsa labarai sun ruwaito Ahmadinejad a birnin Tehran na cewa, zai yi kokarin fadada dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasashen uku, inda za su sa hannu kan wasu yarjeniyoyin da suka jibanci makamashi, cinikayya, al'adu, yawon shakatawa, da kuma kiwon lafiya.
Batun makamashi ya zama wani muhimmin batu cikin ajandar ziyararsa a Jamhuriyar Benin, amma kuma Benin ta ce yayin shawarwari tsakanin Ahmadinejad da takwaransa na Benin Boni Yayi, za su mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi ilmi da ayyukan gona.
Kasar Iran tana bukatar sinadarin uranium a kokarin raya harkokin makamashi, wanda ya janyo ce-ce-ku-ce, amma ministan harkokin wajen kasar Benin Nassirou Arifari Bako ya ce, ziyarar Ahmadinejad a kasashen Benin da Nijar bata da wata alaka da wannan batu. Har wa yau kuma, ya ce, Iran ta samar da tallafin kudi ga gina wani dakin wasan kwaikwayo a jami'ar Abomey-Calavi dake kasar ta Benin.
Bayan da Ahmadinejad ya kammala ziyararsa a kasar Benin, yau ranar Litinin ya tashi zuwa kasa ta biyu a cikin ziyararsa a wannan karo, wato Jamhuriyar Nijar, kasa ce mai arzikin sinadarin uranium a duniya baki daya. Daga baya kuma a ranar Talata mai zuwa, Ahmadinejad zai kai ziyara kasar Ghana, wadda ta kasance kasa ta karshe a cikin ziyararsa a wannan karo. (Murtala)