Ofishin MDD mai kula da 'yan gudun hijira yana aiki kafada da kafada da kasar Nijar don ganin an shawo kan annobar kwalara da ta kunno kai wanda yanzu haka mutane 7 suka mutu, a cewar kakakin MDD lokacin da yake ma manema labarai bayani na duk rana a jiya Talata.
Ofishin babban jami'an majalissar mai kula da 'yan gudun hijira ya sanar a jiyan cewa, an samu barkewar annobar kwalara wanda gwamnatin kasar ta sanar a hukumance a ranar 11 ga wannan watan, kuma yanzu haka mutane 7 sun mutu wadanda suka hada da 'yan gudun hijira daga kasar Mali guda biyu, in ji Eduardo del Buey, mataimakin kakakin babban sakataren MDD.
Barkewar annobar kwalara wani abu ne da ya saba abkuwa a kasar ta Nijar wanda a yanzu haka yake da 'yan gudun hijira kimanin 50,000 daga kasar Mali da kuma wassu guda 31,000 a sansani uku da aka kafa a garin Tillaberi, in ji Mr. del Buey.
Ya zuwa yanzu, an samu rahoton yawan wadanda suka kamu da cutar sun kai 248 a yankin na Tillaberi ,a cikinsu, 31 a sansanin 'yan gudun hijira ne. Don haka, ofishin 'yan gudun hijira na majalissar yana ba da taimako a sansanin 'yan gudun hijira ta hanyar aiwatar da agajin gaggawa na kiwon lafiya da kuma tsabtace muhalli ta hanyar samar da tsabtataccen ruwan sha, yana mai bayanin cewa, akwai bukatar karin magunguna domin tunkarar wadanda za su iya kamuwa da cutar nan gaba.
Cutar kwalara dai, ana iya kamuwa da ita musamman ta hanyar shan ruwa mara tsabta, a shekarar bara, wannan annoba sai da ta kama mutane 5,287, inda guda 110 suka mutu a fadin kasar ta Nijar. Yankin Tillaberi ne ya fi karbuwa da wannan cuta, inda ya samu mutane 4,792 a cikin wannan adadi, sannan 87 daga cikin adadin suka mutu, sai dai babu 'dan gudun hijira da ya mutu a wannan lokacin.
A cikin wata sanarwar da ofishin ya fitar a shafin yanar gizonta, ta ce, tana nan tana aikin ganin ta yada sakonnin wayar da kan jama'a a sansanin 'yan gudun hijiran, sannan kuma za ta yi aiki tare da hukumar kasar da sauran kungiyoyin hadin kai domin shawo kan wannan annobar.
Aiwatar da alluran rigakafi zai zama hadari a ciki da wajen sansanin 'yan gudun hijira, don haka abun lura ne sosai.(Fatimah)