in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon kumbon kasar Sin ya isa tashar da za a harbe shi
2013-04-01 10:37:05 cri

Hukuma mai lura da shirin harba kumbo ta kasar Sin ta bayyana cewa, tuni sabon kumbon kasar mai suna Shenzhou-10, ya isa tashar harbawa dake Jiuquan, ta lardin Gansu a ranar Lahadi 31 ga watan Maris, bayan ya samu nasarar cika sharuddan gwaji kamar yadda aka tsara.

Kumbon wanda ake fatan harbawa sararin samaniya a farkon watan Yuni mai zuwa, ana sa ran zai sauka a na'urar Tiangong-1, domin gudanar da ayyukan kimiyya, da kuma aiko da sakwanni na kimiyya zuwa duniyar bil adama.

Cikin watan Satumbar shekarar 2011 ne dai aka aika da na'urar Tiangong-1 zuwa sararin samaniya, ta kuma sauka kan kumbon Shenzhou na 8 maras matuki a watan Nuwambar shekarar ta 2011, da kuma Shenzhou na 9 mai matuki a watan Yunin bara. Shirin harba kumbon dai, a cewar hukumar, na tafiya yadda ya dace, kuma na'urar Tiangong-1 na cikin yanayi mai kyau, lamarin da zai ba ta damar aikinta yadda ya kamata.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China