in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya nufi Costa Rica, a ci gaban ziyarar da yake yi a Latin Amirka
2013-06-03 13:26:03 cri

A ranar Lahadi 2 ga watan nan da muke ciki ne shugaba Xi Jinping ya kammala ziyarar aiki a kasar Trinidad and Tobago, ya kuma nufi kasar Costa Rica, a ci gaban ziyarar da yake yi a wasu kasashen da ke Latin Amirka. Ziyarar shugaba Xi a Trinidad and Tobago, ita ce ta farko da wani shugaban kasar ta Sin ya kai wannan kasa, tun kafuwar huldar diplomasiyya tsakanin bangarorin biyu a shekarar 1974.

Yayin wannan ziyara, shugaba Xi ya gana da shugaban kasar ta Trinidad and Tobago Anthony Carmona, da kuma firaministan kasar Kamla Persad-Bissessar. Har ila yau, bangarorin biyu sun sanya hannu kan muhimman takardun hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da kuma ilimi. Bugu da kari Xi ya gana da wasu shuwagabannin kasashen yankin Caribbean da suka hada da na Antigua and Barbuda, da Barbados, da Bahamas, da kuma Dominica. Sauran su ne na Grenada, da Guyana, da Suriname da kuma Jamaica. Masu fashi baki dai na ganin wannan ganawa na iya daukaka matsayin dangantakar bangarorin biyu, tare da kawancen dake tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi.

Baya ga Costa Rica, shugaba Xi zai kuma ziyarci kasar Mexico, kafin daga bisani ya isa Amurka, inda zai halarci taron tattaunawa da shugaba Barack Obama a jihar California a ranekun 7 zuwa 8 ga wata. Wannan taron tattaunawa tsakanin jagororin kasashen Sin da Amurka, shi ne irin sa na farko, tun bayan da kasashen biyu suka kammala manyan zabukansu a baya-bayan nan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China