A sanarwar da aka fitar da saukar sa birnin port na spaniya,Shugaba Xi ya ce za'a karfafa hulda da kara ciyar da hadin gwiwwa gaba tsakanin Sin da Trinidad da Tobago wanda hakan ba ma kawai zai amfana ma al'ummomin kasashen biyu ba har ma zai kara hada kai da inganta zumunci tsakanin kasar ta Sin da sauran kasashe na yankin Caribbean dama sauran kasashen dake tasowa.
Shugaban na kasar Sin ya samu tarba daga wajen takwaransa na Trinidad da Tobago Anthony Carmona,da Firaministan kasar Kamla Persad-Bissessar da sauran shugabannin kasar,inda shuagaba Carmona ya shiya wani liyafar maraba ma Shugaban kasar na Sin.
Shugaba Xi wanda shi ne Shugaban kasar Sin na farko da ya ziyarci kasar Trinidad da Tobago tun lokacin da kasashen biyu suka kulla huldar diplomasiyya a shekara ta 1974, ana kuma sa ran zai tattauna da shugaba Carmona da kuma firaminista Persad-Bissessar game da yadda za'a inganta dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen 2.(Fatimah Jibril)