in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya ce Sin za ta yi kokarin inganta dangantakar abokantaka a tsakaninta da Jamhuriyar Congo
2013-03-30 16:20:32 cri

A ranar 29 ga wata a Brazzaville, babban birnin kasar Jamhuriyar Congo, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Jamhuriyar Congo Denis Sassou-N'guesso, inda suka bayyana cewa, kasashen biyu za su yi kokari tare wajen inganta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakaninsu a dukkan fannoni.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin tana dora muhimmanci kan bukatun kasar Jamhuriyar Congo game da hadin gwiwarsu, kuma tana son ci gaba da taimakawa kasar da kuma fara ayyukan hadin gwiwa cikin hanzari. Kasar Sin tana nuna goyon baya ga kamfanonin Sin da su shiga aikin gina wani yankin musamman na tattalin arziki a kasar Jamhuriyar Congo.

A nasa bangare, shugaba Denis Sassou-N'guesso ya ce, kasar Jamhuriyar Congo tana nuna godiya ga kasar Sin domin ta taimakawa kasar a fannin tattalin arziki da kuma zamantakewar al'umma, kuma yana fatan kasarsa za ta kara yin hadin gwiwa tsakaninta da kasar Sin a fannonin gina hanyoyin mota da layin dogo da dai sauransu.

Kana shugaba Sassou-N'guesso ya kara da cewa, kasar Sin tana girmama kasashen Afirka da bada taimako gare su ba tare da tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasashen ba. kuma ra'ayi cewa Sin tana gudanar da mulkin mallaka a nahiyar Afirka ba gaskiya ba ne. Jama'ar kasashen Afirka suna nuna goyon baya ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, kana yana fatan kasar Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da ci gaba a nahiyar Afirka.

Bayan da ya saurari bayanin da shugaba Sassou-N'guesso ya yi game da halin da ake ciki a nahiyar Afirka, shugaba Xi ya nuna cewa, zama tsintsiya madaurinki daya da yin hadin gwiwa tushe ne ga bunkasuwar kasashen Afirka. Kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwa a nahiyar Afirka da kuma nuna goyon baya gare su wajen yin hadin gwiwa don samun bunkasuwa da kansu. Kana ya ce, kasar Sin tana son zama amintacciyar abokiyar kasashen Afirka, da kuma kara inganta sabuwar dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China