Majalisar wadda aka bayyana ta a wani taron manema labarai a Sanaa babban birnin kasar Yemen, ta kunshi tsohon firaministan kasar Abu Bakr Haidar al-Attas da tsohon ministan tsaro Abdullah Eleiwah.
Jami'an adawa dai sun ki yin sharhi kan wannan batu, amma suka ce ba su amince da majalisar ba domin ba ta sanya dukkan bangarorin 'yan adawa a cikin ta ba.
Mai magana da yawun gwamnatin Yemen Abdu al-Janadi kuma mataimakin ministan watsa labarai, ya soki wannan yunkuri da kakkausar murya. Kakakin ya ce yunkurin zai kara ruruta wutar rikicin siyasar kasar.
Al-Janadi ya fada a wani taron manema labarai cewa, shugaba Saleh shi ne halattacen shugaba kuma zai dawo kan mukaminsa cikin 'yan kwanaki sannan wannan majalisa ba za ta maye gurbin gwamnati mai ci ba.
Saleh wanda ke jinya a wani asibitin Saudiya da ke Riyadh sakamakon raunin da ya samu sanadiyar wani harin Bom da aka kaiwa fadarsa a farkon watan Yuni, ya fuskanci bore a kasar baki daya na tsawon watanni 6 inda masu bore ke neman kawo karshen mulkinsa na tsawon shekaru 33, (Ibrahim)