Bisa labarin da wani jami'in mai kula da harkokin cikin gida na kasar Yemen ya bayar, an ce, dakaru masu adawa da gwamnatin kasar sun fara bude wuta ga sojoji da ke sintiri, alamarin da ya haddasa musanyar wuta a tsakanin bangarorin biyu, kuma sojojin gwamnatin kasar sun tura sojoji da dama zuwa yankin Hassaba.
Tun daga ran 4 ga wata da dare, an kara shiga hali mai tsanani a wannan yanki, saboda dakaru masu adawa da gwamnatin kasar sun hana wasu sojojin gwamnatin kasar shiga wannan yanki.
Bisa labarin da wadanda suka ganewa idonsu lamarin suka bayar, an ce, rikicin ya yi sanadiyyar raunanta mutane da yawa, daga cikinsu akwai fararen hula, amma babu wanda ya mutu a sakamakon rikicin.(Abubakar)