Shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh ya yi jawabi a ran 25 ga wata, inda ya nuna maraba da kuduri mai lamba 2014 da kwamitin sulhu na MDD ya gabatar game da batun Yemen.
Ali Abdullah Saleh ya ce, jam'iyyar da ke kan karagar mulkin kasar Yemen ta shirya sosai na sake farfado da shawarwari tare da jam'iyyar adawa, kuma za ta kafa tsarin da ya dace tare da kungiyar GCC ta kasashen Larabawa domin kulla yarjejeniya tun da wuri. Bayan da aka kulla yarjejeniyar shiga tsakani, za a gudanar da babban zabe kafin lokacin da aka tsara.
A ran 21 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri, inda aka nemi bangarori daban daban na kasar Yemen da su dakatar da tada tarzoma, kuma an yi kira ga shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh da ya kulla yarjejeniyar da kungiyar GCC tun da wuri. Gwamnatin kasar Yemen ta bayar da sanarwa a ran 22 ga wata cewa, za ta kula da harkokin wannan yarjejeniya yadda ya kamata.(Lami)