in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan adawa a Yemen sun bukaci sojojin da suka canja sheka, kabilun kasar da su kare matakin kin jinin gwamnatin kasar
2011-08-25 14:28:45 cri

A ranar Laraba ne 'yan adawan Yemen suka zargi shugaba Ali Abdullah Saleh da kokarin daukar matakin soja don kawo karshen boren da ake yi a kasar, inda suka yi kira ga sojojin da suka juya baya ga gwamnati da kabilun kasar masu dauke da makamai, da su kare matakin kin jinin gwamnatin kasar da aka dauka.

Kakakin gungun taron hadin gwiwar jam'iyyun adawa na kasar Mohamed Qahtan ya shaida wa kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, shugaba Ali Abdullah Saleh da 'yan uwansa suna shirin daukar matakin soja don kawo karshen watannin da aka dauka ana boren neman Saleh ya sauka daga mulki.

Qahtan ya ce, Saleh ya yanke shawarar fuskantar kalubalen jama'ar da ke son ya sauka daga karagar mulki, dan haka muna kira ga sojojin da suka juya baya ga gwamnati, kalibun kasar masu dauke da makamai wadanda suka yi alkawarin kare dakarun juyin-juya hali, da su cika alkawuransu.

A halin da ake ciki kuma wasu ganau sun bayyana cewa, dubban masu kin jinin gwamnati sun gudanar da gangami a ranar Laraba a wasu manyan biranen kasar, ciki har da Sanaa da Taiz, birni mafi girma a kasar don murnar nasarar da al'ummar ta Yemen suka samu.

A farkon watan Yuni ne aka tilasta wa Saleh da wasu jami'an kasar 87 yin jinya a kasar Saudiya bayan wani bom din daya fada kan fadar shugaba Saleh a Sanaa.

A ranar Talata ne firaministan kasar Yemen Ali Mohammed Mujawar wanda ya murmure daga raunin harin bom din watan Yuni ya iso birnin Sanaa. Kana kamfanin dillancin labarum kasar Saba ya ruwaito Mujawar na cewa, nan ba da dadewa ba shugaban da sauran jami'an da suka ji rauni za su dawo Yemen. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China